Jagoran jam’iyyar APC Bola Ahmed Tinubu ya yi alkawarin cewa zai kawo karshen matsalar tsaro a Najeriya idan aka zabe shi matsayin shugaban kasa.
Tinubu, ya yi wannan alkawarin ne a ranar Asabar lokacin da yake zantawa da dimbin matasan jam’iyyar APC a filin wasa na Mobalaji Johnson da ke Onikan, jihar Legas.
“Hadin kan Najeriya shi ne burinmu,” in ji Mista Tinubu.
“Mun yi muku alkawari, za mu sadaukar muku da kanmu don goben kasar mu ta yi kyau.”
Ya ce ya fito ne domin ya wakilci matasa, inda ya ce ta hanyar hadin kai ne kawai Najeriya za ta iya cimma burinta.
“Ina so in zama shugaban kasa a gare ku, domin na yi tanadin kafa sabuwar Najeriya mai cike da zaman Lafiya da kwanciyar hankali.” in ji shi.
Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, wanda ya tsaya kusa da Tinubu a wajen gangamin na ranar Asabar, ya ce matasan yankin Kudu-maso-Yamma sun nuna jajircewa wajen yakin neman zaben shugabancin kasar na Tinubu.
Ya bayyana hakan ne a jerin sakonnin da ya wallafa a shafinsa na Twitter bayan taron.










































