Gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya umarci duk wani mai rike da mukamin siyasa a gwamnatinsa da ke da muradin tsayawa takara a zaben shekarar 2023, da ya gaggauta sauka akan mukamin sa nan da ranar 18 ga watan Aprilun 2022.
Wannan na kunshe ne cikin wata sanar da sakataren yada Labaran gwamnan Abba Anwar ya fitar.
Jaridar Solacebase ta rawaito Abba Anwar na cewa umarnin ya biyo bayan yin biyayya ga sashi na 84 (12) sha biyu cikin baka na sabuwar Dokar zaben da aka yiwa gyara a shekarar 2022.













































