Lugudan wuta ya yi sanadiyar mutuwar akalla mayakan ISWAP 70-NAF

IMG 20220417 WA0000
IMG 20220417 WA0000

Rundunar sojin saman Najeriya ta sanar da cewa ta hallaka ‘yan kungiyar ISWAP sama da 70 a yankin tafkin Chadi da ke kan iyaka da Jamhuriyar Nijar.
A wata sanarwa da mai Magana da yawun rundunar sojin saman, Edward Gabkwe ya fitar, ya ce jiragen saman Najeriya da Nijar ne suka gudanar da atisayen hadin gwiwa.
Yankin na tafkin Chadi da Najeriya ta ce ta kaddamar da lugudan wuta ta sama yanki ne da tun tuni mayakan kungiyar suka maida shi sansanin su tun shekarar 2016.
Sanarwar ta ce, “Lugudan wutar da aka yi a yankin tun a ranar 13 ga Afrilun 2022, an gano wasu ‘yan ta’adda, wadda da alama masu ikirarin jihadi ne.”
A dalilin haka ne suka kai hare-hare ta sama a ranar 14 ga watan Afrilu a Tumbun Rego da kuma wani sansanin horo da ke kusa, inda suka yi amfani da jiragen saman kasashen Najeriya da Nijar, in ji sanarwar.
“Sama da ‘yan ta’addar ISWAP 70 an kawar da su, wasu kuma sun ji munanan raunuka,” in ji Edward.
Sojoji sun shafe fiye da shekaru 12 suna gwabza yaki da ‘yan ta’addar masu ikirarin jihadi.
Tun a shekarar 2021, mayakan ISWAP suka mamaye yankin bayan da shugaban kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau ya mutu a rikicin kabilanci, Shekau dai ya shahara a duniya bayan sace ‘yan mata kusan 300 a garin Chibok tun a shekarar 2014.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here