Kungiyar Tuntuba ta Arewa bata da wani Reshen Matasa-Jagoran ACF

Arewa Consultative Forum 1 678x381 1
Arewa Consultative Forum 1 678x381 1

Kungiyar tuntuba ta Arewa ACF ta nesanta kanta da wata kungiya da ake kira da kungiyar matasan Arewa, inda ta ce a karkashinta ba wani reshen matasa.

Jagora a kungiyar ta ACF Alhaji Musa Saidu, kuma shugaban kungiyar Yan Arewa mazauna Kudancin Najeriya, shi ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya ranar Lahadi a Fatakwal.

Saidu, wanda shi ma dan kungiyar ACF ne kuma Danburam na Fatakwal, ya ce kungiyar da ake kira ta Matasan Arewa ba a doron doka aka kafata ba.

“Ina so na sanar da al’umma kowa da kowa batare da wata fargaba ko tsoron sanya shakku a zukatan al’umma ba, cewa Kungiyar tuntuba ta Arewa bata da wani reshen matasa a karkashinta, kuma ni din nan ina daya daga cikin wadanda suka kafa Kungiyar tuntuba, babu wani lokaci da muka kaddamar da wani reshe karkashin kungiyarmu”. Inji Saidu.

“Ina wadannan jawabai ne sakamakon wasu labarai dake yawo a fadin kasar nan cewa, akwai wata kungiyar Matasan Arewa dake zuwa wajen ‘Yan siyasa, musamman na yankin Kudu da sunan Maula, kuma suna ikirarin su ‘Yan Kungiyar Matasan Arewacin Najeriya ne”.

Saidu ya kuma bukaci ‘Yan siyasar Najeriya musamman na yankin kudancin Kasar da su yi watsi da duk wasu matasa da suka je musu da sunan Kungiyar Matasan Arewa, domin kuwa basu da rijista a hukumance.

Ya kuma bukaci hukumomin tsaro dasu gayyaci Mambobin waccan kungiyar domin kuwa ‘Yan damfara ne da suka damfarar dai-daikun mutane kawai don su tara kudi.

“Maimakon su rinka zuwa Maula yafi kyautuwa, su yi tunanin sana’o’in dogaro da kai domin su tsira da mutuncinsu, wadanda kuma suka yi karatu mai zurfi a cikinsu su nemi ayyukan Gwamnati ko kuma na bangarori masu zaman kansu ya fiye musu wannan galantoyin”.

“Yan uwanmu dake yankin kudu maso gabashin Najeriya sun fi maida hankali wajen sana’o’in su, haka suma yan uwanmu Yarbawa sun fi mayar da hankali kan sana’o’in su na hanu kamar gyaran mota da babura”.

“Amma mu matasanmu na arewa sun fi sha’awar tara kudi cikin gaggawa, wannan dalili ne yasa wasunsu kiran kansu da Kungiyar Matasan Arewa”.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here