Tsohon shugaban karamar hukuma da wasu 4 sun mutu a rikicin da ya barke a jihar Osun

Riot

Kimanin mutane biyar ne suka rasa rayukansu a rikicin da ya barke bayan yunkurin karbe sakatarorin kananan hukumomi da jami’an siyasar jam’iyyar adawa ta APC suka yi a ranar Litinin a jihar Osun.

Daya daga cikin wadanda suka mutu a rikicin da ‘yan barandan jam’iyyar APC da jam’iyyar PDP mai mulki suka yi, akwai tsohon shugaban karamar hukumar Irewole, Ikire, Mista Remi Abass.

Sauran kuma a cewar kwamishinan tsare-tsare da harkokin gwamnati na jihar Osun, Soji Ajeigbe sune Damilare Oloyede da Taye, wadanda ake zargin an harbe su a kananan hukumomin Iragbiji da Boripe na jihar.

Ajeigbe, yayin da yake zantawa da manema labarai a Iragbiji, ya yi zargin cewa jami’an jam’iyyar adawa ta APC sun kashe Damilare da Taye wadanda ‘yan PDP ne a kusa da sakatariyar karamar hukumar Boripe a Iragbiji.

Karin labari: Shehu Sani ya yi martani ga jami’an tsaro na Anambra kan barazanar kama matan da aka gani ba tare da rigar Mama da wando ba

Da yake yiwa manema labarai karin haske a sakatariyar jam’iyyar APC da ke Osogbo, Alhaji Jamiu Olawumi, ya zargi ‘yan jam’iyyar PDP mai mulki da kashe ‘ya’yan jam’iyyar APC guda uku da suka hada da Abass, kansilan karamar hukumar Olaoluwa da ba a bayyana sunan sa ba da kuma wani dan APC daga karamar hukumar Isokan.

Olawumi ya kuma tabbatar da cewa a kasa da goma sha biyar daga cikin kotun daukaka kara sun mayar da shugabannin kansilolin da karfe 9 na safe, yayin da karfe 9:30 na safe, kusan dukkan sauran shugabannin kansilolin sun karbi mukamin sai wasu ‘yan PDP suka kore su daga baya.

APC ta sha alwashin cewa duk zababbun shugabannin jam’iyyar da kotun daukaka kara ta yanke ranar 10 ga watan Fabrairu, 2025 za su ci gaba da tafiya ofis kamar yadda kotun daukaka kara ta umarta.

Rikici ya barke a kusan dukkanin kananan hukumomin jihar a safiyar ranar Litinin yayin da shugabannin kansilolin da aka kora suka yi yunkurin karbar mukamansu bayan hukuncin kotun.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here