Gwamnan Kano ya aike wa da Majalisa sunan Murtala Garo don tantance shi a matsayin mataimakin gwamna

Screenshot 20260422 054727

Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya aike wa da Majalisar dokokin jihar sunan Alhaji Murtala Sule Garo domin tantancewa tare da tabbatar da shi a matsayin mataimakin gwamnan jihar Kano.

A wani sako da sakataren watsa labaran gwamnan, Mustapha Muhammad ya sanyawa hannu, ta ce gwamnan ya yi hakan ne dogaro da sashi na 191(3) na kundin tsarin mulkin kasa 1999 da aka yiwa kwaskwarima, wanda ya baiwa gwamnan damar nada mataimakin na shi domin cike gurbi.

Jaridar SolaceBase ta rawaito kujerar ta mataimakin gwamnan ta kasance babu kowa, biyo bayan ajiye aiki da tsohon mataimakin gwamna Comrade Aminu Abdussalam Gwarzo yayi a ranar 27 ga watan Maris.

Bayan doguwar tattaunawa da masu ruwa da tsaki, gwamnan ya bukaci majalisar da ta sahale nadin na Garo.

A cewar sanarwar, Murtala Sule Garo mai shekarar 48 gogaggen dansiyasa ne da ya shafe sama da shekara ashirin yana siyasa a matakai da dama na zababbe da kuma nadi.

Cikin mukaman da ya rike, Murtala ya taba zama sakataren shirye-shiryen jam’iyya, ya kuma taba zama mashawarci na musamman ga gwamna Kano kafin daga bisani a zabe shi a matsayin shugaban karamar hukumar Kabo.

Ya kuma taba zama shugaban shugabannin kananan hukumomi na jihar Kano, sannan ya zama kwamishinan kananan hukumomi da al’amuran masarautu, yayin da zaben 2023 ya yi takarar mataimakin gwamna a jam’iyyar APC.a

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here