Mashawarci na musamman ga ministan kan yada labarai da wulda da Juma’a, Tunji Bolaji ne ya sanar da matsayar ministan, inda yace ministan lantarkin Adebayo Adelabu, zai sanar da hakan cikin kwanaki masu zuwa.
Ya kuma ce ministan ya nemi amincewar shugaban kasa Bola Tinubu kafin daukar wannan mataki, ya kuma bayyana masa aniyarsa ta yin takarar gwamna a jihar shi.
Bolaji, ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba a Abuja, inda yace ministan zai sauka daga mukamin na sa ne domin baiwa bangaren na lantarki damar ci gaba da gudanar da aiki ba tare da wani tsaiko ba, wanda shi ne abu mafi muhimmanci.
A cewar shi, Adelabu ya gana da shugaban kasa Bola Tinubu a ranar Talata a radar shugaban kasa dake Villa a Abuja, inda ya gabatar masa da cikakken rawoto a bangaren wutar lantarki cikin shekara biyu da rabi da yayi a ma’aikatar.
Shugaban kasar ya yaba wa ministan kan irin namijin kokarin da yayi da kuma sadaukarwar da ya yi musamman irin shirin da ya samar a bangaren lantark. Shugaban kasar ya kuma gode wa ministan tare da yi masa fatan alheri a takarar da yake yi ta gwamna.
A nasa bangaren, ministan ya nuna matukar jindadin shi tare da gode wa shugaban kasar bisa damar da ya bashi ya yi aiki wa kasa.












































