Indonesia za ta tsaurara hukunci kan mazinata

317931455 10161009078517608 3484613763696158801 n
317931455 10161009078517608 3484613763696158801 n

Majalisar dokokin Indonesia na shirin amincewa da wata doka ta hukunta mazinata, inda za a iya ɗaure mutum tsawon shekara guda idan aka same shi da laifi.

Sabbin dokokin za su ƙunshi dokar da za ta haramta cin fuskar shugaban ƙasa ko gwamnati, da kuma bayyana ra’ayin da ya ci karo da muradan ƙasar.

Haka nan ana haramta zamantakewar namiji da mace ba tare da aure ba..

Ƙaramin ministan shari’a na ƙasar ya shaida wa Reuters cewa a ranar 15 ga watan Disamba ne ake sa ran majalisar za ta amince da sabbin dokokin, bayan kwashe shekaru ana aiki a kansu.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here