Shugaba Bola Tinubu ya dakatar da ministar ma’aikatar jin kai, Dakta Betta Edu, ba tare da bata lokaci ba.
Wata sanarwa da mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai, Ajuri Ngelale ya fitar, ta ce dakatarwar ta biyo bayan alkawarin da ya dauka na tabbatar da daidaito da gaskiya da rikon amana a cikin tafiyar da mulkin talakawan Najeriya.
Karanta wannan:Tinubu ya bada umarnin yin bincike a ma’aikatar jin-kai kan zargin almundahana
Sanarwar ta ce, “Shugaban ya kuma umurci Shugaban Hukumar EFCC da ya gudanar da cikakken bincike a kan duk wani abu da ya shafi hada-hadar kudi a ma’aikatar jin kai ta tarayya, da kuma sauran hukumomin da ke karkashinta.
Cikakken bayanin…..
A daidai lokacin da ya sha alwashin tabbatar da gaskiya da rikon amana a cikin tafiyar da mulkin talakawan Najeriya, shugaba Bola Tinubu ya dakatar da ministar ma’aikatar jin kai Dakta Betta Edu daga mukaminta ba tare da bata lokaci ba.
Shugaban ya kuma umurci Shugaban Hukumar EFCC da ya gudanar da kwakkwaran bincike kan duk wani abu da ya shafi hada-hadar kudi a ma’aikatar jin kai ta tarayya, da kuma sauran hukumomin da ke karkashinta.
An umarci ministar da aka dakatar da ta mikawa babban sakataren ma’aikatar aiki, sannan kuma shugaban kasa ya umarce ta da ta baiwa hukumomin bincike cikakken hadin kai yayin da suke gudanar da bincike.
Bugu da kari, shugaban kasar ya sanya wani kwamitin da ke karkashin jagorancin ministan harkokin tattalin arziki da kuma ministan kudi domin gudanar da cikakken bincike kan hada-hadar kudi da tsare-tsaren zuba jari da nufin yin garambawul ga tsarin tattalin arziki.
Duka wadannan umarnin na shugaban kasa zasu fara aiki ne nan take.
Chief Ajuri Ngelale
Mai bawa shugaban kasa shawara na musamman, kan harkokin yada labarai
8 ga Janairu, 2024












































