Shugaba Bola Tinubu ya bayar da umarnin yin cikakken bincike a ma’aikatar jin kai wadda Betta Edu ke jagoranta kan zargin badakalar kudade.
Ministan yada labarai, Mohammed Idris shi ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi.
Karanta wannan: Gwamatin tarayya ta ayyana Litinin a matsayin ranar hutu
musayar miyau ta barke a ma’aikatar ne bayan zargin cewa ministar jin kai Betta Edu ta bayar da umarnin tura kudi kimanin naira miliyan 585 zuwa asusun banki na wata mata.
Sanarwar da ministan yada labarai ya fitar, ta ce ta samu labarin abin da ke faruwa a ma’aiktar ta jin kai a karkashin Betta Edu, inda ya ce gwamnati ta kuduri aniyar yin bincike don fito da gaskiya.
Karanta wannan: Shugaban kasa Bola Tinubu ya rattaba hannu kan kasafin bana
Idris ya ce gwamnati ta kuduri aniyar bankado gaskiyar lamarin, tare ba da tabbacin cewa za a dauki matakin da ya dace don ganin an hukunta wadanda aka samu da laifi.
Ministan yada labaran kasar ya ce za a sanar da sakamakon binciken ga yan Najeriya.
Umarnin gudanar da bincike da shugaba Tinubu ya bayar, na zuwa ne bayan fitar wata takardar biyan kudi da ministar ta aike wa ofishin babbar akanta janar ta kasar, inda a ciki take bukatar a tura zunzurutun kudi har naira miliyan 585, 189,500, don biyan tallafi, a wani bangare na tallafa wa masu tsananin bukatar tallafi a wasu jihohin kasar hudu.
Karanta wannan: EFCC ta kama shugabar hukumar NSIP, Halima Shehu
To sai dai wani abu da ya ja hankali game da biyan kudaden shi ne sunan asusun bankin da aka biya kudin na wata mata ce mai suna Onlyelu Bridget Mojso.
Tuni dai ofishin babbar akanta janar ta kasar ya ce ba ya biyan kudin gudanar da wani aiki na gwamnati a asusun wani mutum.













































