Gwamatin tarayya ta ayyana Litinin a matsayin ranar hutu

Rauf Aregbesola. 2
Rauf Aregbesola. 2

Gwamanatin tarayya ta ayyana ranar Litinin, daya ga watan Mayu a matsayin ranar hutu, domin bikin ranar ma’aikata.

Ministan harkokin cikin gida,Rauf Aregbesola, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da sakataran ma’aikar cikin gida, Shuaib Belgore ya sanyawa hannu a ranar Juma’a.

Ministan ya yabawa ma’aikata bisa sadakauwar da suke tare da aiki  ba ji ba gani domin cigaban kasa Najeriya.

Ya kuma jin-jinawa jami’an tsaro bisa tarin nasarorin da suka samu wajan yaki da ta’addanci a fadin kasa baki daya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here