Rundunar sojin saman kasar nan ta ce kokarin da dakarun rundunar na Operation Hadin Kai ke yi na wanzar da tsaro a yankin Arewa maso Gabas, na ci gaba da samun nasara.
Daraktan yada labarai na rundunar AVM Edward Gabkwet ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi a Abuja.
Karanta wannan: Rundunar Sojin sama ta yi Karin girma ga jami’anta
Gabkwet ya ce daya daga cikin irin wannan nasarorin da aka samu ya faru ne a ranar 5 ga watan Janairu, a garin Parisu, bayan da ‘yan ta’adda suka kwashe kwanaki suna tafiya da kayan da ake zargin makamai ne da alburusai zuwa yankin.
Ya ce, Parisu, wani wurin da ke kusa da dajin Sambisa, ya kasance wani yanki na ‘yan ta’adda da ba kowa bayan da sojojin nasu suka yi nasarar kawar da ayyukan ‘yan ta’addan.
Karanta wannan: Rundunar Sojin Najeriya ta dauki alhakin harin da aka kai Jihar Kaduna
Ya ce haduwar ‘yan ta’addan a wurin ya sanya ake zargin aniyarsu da shirinsu, don haka aka ba da umarnin kai farmaki wurin.
A cewarsa, sakamakon hare-haren ya haifar da wata babbar gobara daga wurare biyu da ke kusa da wajen, yayin da wasu ‘yan ta’addan da suka tsira suka yi ta gudu domin tsira da rayukansu.
Karanta wannan: Gwamnatin jihar Yobe ta soke lasisin makarantu masu zaman kan su
Gabkwet ya ce, a wani aikin leken asiri ta sama a ranar 2 ga watan Janairu, wani jirginsu ya kai hari ga wasu wurare a Tumbun Alura.
Ya ce yayin liken asirin an ga wasu kwale-kwale guda uku, dauke da wasu kaya da ake zargin muggan ne.