‘Yan-kasuwa sun koka da yadda Jami’an tsaro a Kebbi ke karbar kudi a hannun su

Kebbi Map 750x430
Kebbi Map 750x430

‘Yan-kasuwa da Manoma da ke tafiya ta garin Bagudo a karamar hukumar Bagudu a jihar Kebbi sun koka da yadda jami’an tsaro ke karbar kudi ba kakkautawa a shingayen binciken ababen hawa da ke kan tituna.

Hanyar da ta hada Najeriya da Jamhuriyar Benin.

“Daga Kasuwar Tsamiya, da ake sayar da hatsi, idan babbar mota dauke da buhunan masara ko gero 600 ta taho sai an biya kudin da bai gaza Naira 600,000 ba sannan za’a bar mai kayan ya isa Argungu da Birnin Kebbi.

Karanta wannan: Shugaban karamar hukuma ya mutu a jihar Kebbi

Ya kuma danganta hauhawar farashin amfanin gona da kayayyaki da sauran muhimman abubuwan da ake samu a kan karbar kudaden da jami’an tsaro ke yi a yankin.

Ya bukaci gwamnatin jihar da ta aiwatar da tsarin tattara kudaden shiga na cikin gida da kuma hana karbar kudadfe ba bisa ka’ida ba.

Karanta wannan: Gwamnatin Zamfara ta fayyace dalilan rufe wasu kasuwannin dabbobi a jihar

Shi ma a nasa jawabin shugaban kungiyar Alhaji Rabi’u Mainasara ya koka da yadda ake karbar kudaden.

Mainasara ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta jihar Kebbi, da kuma shugabannin hukumomin tsaro da abin ya shafa da su sa baki don dakatar da wannan lamari.

A nasa bangaren, kansila a yankin, Alhaji Abubakar Usman Tsamiya, ya koka da yadda mazauna yankin suka fusata da karbar kudin.

Karanta wannan: Sojoji sun ceto mutane 52 da aka yi garkuwa da su a Sokoto

Da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Nafi’u Abubakar, yace ba su da masaniya game da karbar kudin amma ya ce za a gudanar da bincike.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here