Kylian Mbappe ya cimma Yarjejeniyar tafiya da Real Madrid

Mbappe
Mbappe

Kylian Mbappe, ya cimma yarjejeniyar tafiya Real Madrid a karshen kwantiraginsa da Paris St-Germain.

Sai dai kudin da Madrid din za ta biya Mbappe, wanda wa’adinsa a PSG zai kare a bazaran nan mai zuwa bai kai yawan wanda suka yi masa tayi ba a tattaunawarsu ta 2022.

Amma kuma duk da wannan yarjejeniya Mbappen zai iya sauya shawara ya tafi gasar Premier.

Karanta wannan: Manchester City Ta Yiwa Real Madrid Raga-Raga A Wasan Kusa Da Na Karshe

Juventus ta fice daga zawarcin dan wasan tsakiya na Manchester City Kalvin Phillips na Ingila saboda kudin da aka tsuga na bayar da shi aro da kuma yawan albashin da za a ba shi.

Wannan janyewa da Juventus ta yi za ta iya karfafa wa Newcastle damar samun dan wasan mai shekara 28.

Karanta wannan: Tsohon dan kwallon Brazil Mario Zagallo ya mutu

Liverpool za ta iya tsintar dami a kala idan Al-Ettifaq ta Saudiyya ta yanke shawarar sayar da dan wasanta na tsakiya Jordan Henderson na Ingila.

Everton ta sanya farashin fam miliyan 60 a kan Amadou Onana, wanda kuma ake ganin Arsenal na son sayen matashin dan wasan na tsakiya na Belgium mai shekara 22.

Karanta wannan: Kano Pillars Ta Dauki Sabbin ’Yan Wasa 22

Chelsea, da Manchester United da kuma AC Milan na sa ido a kan dan bayan Nice da Faransa Jean-Clair Todibo, amma kuma kungiyar ta Faransa na fatan rike shi a lokacin kasuwar ‘yan wasa ta watan nan na Janairu.

Wasu bayanai na cewa an bai wa Barcelona damar sayen tsohon dan wasan tsakiya na Manchester United da Ingila Jesse Lingard.

Dan wasan mai shekara 31 ba shi da kungiya tun bayan da ya bar Nottingham Forest a karshen kakar bara.

Dan gaban Ingila Ivan Toney, ya ce yana da sauran aikin da yake so ya kammala yayin da yake shirin dawowa wasa a Brentford bayan dakatar da shi da aka yi tsawon wata takwas daga taka leda bayan saba dokokin caca.

Juventus za ta fara tattaunawa da dan wasanta na tsakiya Weston McKennie, Ba’amurke mai shekara 25 kan tsawaita kwantiraginsa.

West Ham za ta nemi sayen dan bayan Wolves Max Kilman, dan Ingila idan ta samu kudi daga cinikin dan bayanta na Moroko Nayef Aguerd, a watan nan.

Dan wasan tsakiya na Newcastle Sean Longstaff ka iya barin kungiyar idan har aka samu kungiyar da ta saye shi da kima.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here