Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal na dab da rasa damarta kan mafarkin da take na lashe gasar Premier a kasar Ingila.
Hakan na zuwa ne sakamakon rashin nasarar da ta yi da ci 1-0 a hannun kungiyar kwallon kafar West Harm United.
Kungiyar ta Arsenal dai ta yi rashin nasarar ne a gidanta a wasan mako na 26 na gasar da aka buga a ranar Asabar 22/02/2025.
Karin karatu: EPL- Arsenal ta ragargaza Manchester City da ci 5-1
Dan wasan West Harm Jarrod Bowen ne dai ya zura kwallon a mintuna na 44 dab da za a tafi hutun rabin lokaci.
A mintuna na 73 ne alkalin wasa ya baiwa dan wasan kungiyar ta Arsenal Myles Lewis-Skelly katin kora sakamakon laifi da ya yi a wasan.
Yanzu haka dai Arsenal ta ci gaba da zama a matakin da take na 2 da maki 53 wanda hakan yasa Liverpool dake a matsayin ta 1 da maki 61 ta bata tazarar maki 8.