Neman Tikitin buga gasar cin kofin Duniya: Najeriya ta doke kasar Rwanda

Super Eagles sabo 750x430

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Najeriya Super Eagles ta dole ƙasar Rwanda da ci 1-0 a gasar neman cancantar buga gasar cin kofin Duniya.

An dai fafata wasan ne ranar Asabar 06/09/2025 a filin wasa na Uyon jihar, Akwa Ibom.

Dan wasa Tolu Arokodare ne ya zurawa Najeriya ƙwallon da y bata nasara a kan Ƙasar ta Rwanda a mintuna na 51 bayan dawowa daga hutun rabin lokaci.

Karanta: Tawagar Super Falcons Sun Iso Najeriya

Nasarar da Najeriya ta samu kan ƙasar ta Rwanda ya sanya tana da maki 10 a rukunin D da take bayan buga wasa 7 da ta yi.

Yanzu dai Najeriya za ta ziyarci ƙungiyar Bafana-Bafana da ke ƙasar Afrika ta Kudu da take da maki 16 a rukunin inda ƙasar Benin Republic take a matakin ta 2 da maki 11 yayin da Najeriya take a matsayin ta 3 da maki 10.

Karin karatu: Oshiola ta sanya kwantaragin shekaru da kungiyar Al-Hilal ta Saudi Arabiya

Yanzu haka dai Najeriya za ta ziyarci ƙasar Afrika ta Kudu a ranar Lahadi dan buga wasanta na uku kuma ya zama dole ta samu nasara a wasan idan har tana san samun Tikitin buga gasar cin Kofin Duniya da za a gabatar a shekarar 2026 mai kamawa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here