Tawagar Super Falcons ta Najeriya sun sauka a Najeriya daga kasar Morocco inda suka lashe gasar cin kofin Afrika na mata karo na 10.
Tawagar ta isa filin tashi da saukar jiragen sama na Nnamdi Azikiwe dake Abuja a cikin wani jirgin da misalin karfe 2:26 na rana.
Tawagar ta sami gagarumin tarba daga magoya bayanta da jami’an gwamnati, wadanda wasunsu sun shafe sa’o’i a filin jirgin saman domin tarbar jaruman nasu.













































