Yar wasan gaban Nigeria da kungiyar kwallon ƙafa ta Bay FC da ke ƙasar Amurka Asisat Oshoala ta sanya hannu kan kwantaragin shekaru 2 da kungiyar ƙwallon ƙafar Mata ta Al-Hilal da ke kasar Saudi Arabiya.
A ranar Litinin 1 ga watan Satumbar 2025 ne dai kwantaragin Oshiola mai shekaru 30 ya ƙare da ƙungiyar Bay FC, inda ta gudanar da gwajin Lafiya a birnin Riyadh na ƙasar ta Saudiyya kamar yadda Jaridar ESPN ta rawaito a shafinta na Instagram.
Zakarar ƴar wasan Afrika karo biyu, ta nuna jin dadinta bisa sanya hannu kan kwantaragin da ta yi da kungiyar ta Al-Hilal.
Ta dai kwashe shekaru biyar a ƙungiyar Barcelona da ke kasar Spain Inda ta zura mata ƙwallaye 107 cikin wasanni 149 da ta buga, inda ta lashe mata gasar kwallon kafar Mata ta ƙasar guda 5 da ta zakarun Turai guda 2.
Karin karatu: Yan wasan Najeriya sun lallasa na Kamaru da ci 2-0 a wasan sada zumunta
Haka zalika ta buga wasa a ƙungiyar Arsenal da Liverpool, da ke kasar England da kuma Dalian Quanjian dake ƙasar Chana bayan ta kammala wasa da ƙungiyoyin ƙwallon ƙafar gida Najeriya na Robo da kuma Rivers Angels.
Yanzu haka dai Oshiola za ta buga wasa da abokanan ƙwallonta a ƙungiyar ƙwallon ƙafar Mata ta Najeriya Super Falcons Ashleigh Plumptre da kuma Francisca Ordega.
Kungiyar Al Hilal dai ta kammala kakar wasannin gasar kofin kwallon kafar Mata ta kasar Saudi Arebiya a matakin ta 6.













































