Jagoran jam’iyyar APC kuma dan takarar shugaban kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya taya tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar murnar zama dan takarar jam’iyyar adawa ta PDP, bayan zaben fidda gwani da aka gudanar a filin wasa na Moshood Abiola da ke Abuja jiya Asabar.
A cikin wata sanarwa da Daraktan yada labarai na kwamitin yakin neman zaben Tinubu, Bayo Onanuga, ya fitar, Tinubu ya yabawa Atiku bisa kishin kasa da jajircewarsa na niyyar ciyar da Najeriya gaba.
“Tinubu ya kuma taya sauran ’yan takarar murna bisa yadda suka gudanar da zabensu cikin tsari da lumana tare da yin alkawarin yin gangamin zagaye tare da wanda ya yi nasara, bisa gaskiya,” in ji sanarwar.
Ya yi fatan tsohon mataimakin shugaban kasa, wanda kuma shi ne dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP a 2019, zai zama abokin hamayyarsa, da yardar Allah da goyon bayan wakilan APC, a zaben shugaban kasa mai zuwa na 2023.
Jagoran jam’iyyar APC na kasa ya ce nasarar da Atiku ya samu bai ba ‘yan Najeriya mamaki ba la’akhari da gogewarsa da kuma dadewarsa yana neman takarar shugaban kasa tun daga 1993.
A yayin da yake maraba da dan takarar jam’iyyar PDP a zaben, Tinubu ya kara da cewa ya kamata zabe mai zuwa ya kasance kan batutuwan da za su inganta rayuwar ‘yan Najeriya da suka hadar da kawo zaman lafiya da ci gaba baya ga kwanciyar hankali da warware dimbin kalubalen zamantakewa da rashin tsaron da kasar ke fuskanta a halin yanzu.













































