Tsohon gwamnan Jihar Kano Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya lashe zaben fitar da gwanin takarar shugabancin Kasa a jam’iyyar NNPP.
Tsohon Sanatan, ya lashe zaben fitar da guda cikin masu bukatar tsayawa takarar shugabancin kasar a jam’iyyar mai kayan dadi (wato NNPP) bayan da Wakilan jam’iyyar 774 daga jihohin Najeriya 36 ciki har da birnin tarayya Abuja suka zabe shi ta hanyar Yar tinke.
Jaridar Solacebase ta rawaito cewa har kawo lokacin rubuta wannan rahoto jam’iyyar ta NNPP ta ci gaba da gudanar da taronta a filin wasa na Mashood Abiola dake Abuja.













































