Yanzu-yanzu: Real Madrid ta lashe kofin Zakarun turai karo na 14 bayan doke Liverpool

IMG 20220529 WA0000
IMG 20220529 WA0000

Real Madrid dake kasar Spain, ta zama Zakaran gasar kofin zakarun Turai na Uefa Champions league.

A wasan karshen da aka fafata ranar Asabar 28 ga Mayu 2022, a babban filin wasa na Stade de France dake birnin Paris na kasar Faransa Madrid ta yi galaba akan Liverpool da ci 1-0.

Dan wasa Vinicius Junior, ne ya saka kungiyar ta Madrid a gaba, kana kwallon da ta bata nasara a minti na 59, zagaye na biyu bayan samun taimako daga hannun Dan wasa Federico Valvarde.

Da nasarar da ta samu tawagar ta Madrid, ta kafa tarihin lashe kofin mafi rinjaye fiye da kowacce kungiyar a Turai har sau 14, inda Ac Milan ke rufa mata baya da ta dauka sau 7, ya yinda Liverpool din da suka fafata wasan karshe take da nasara 6, ita da Bayern Munich.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here