Da ɗumi-ɗumi: An sanya dokar hana fita ta sa’o’i 24 bayan tabbatar da mutuwar mutane 3 a rikicin Bauchi

Burnt car in Bauchi
Burnt car in Bauchi

Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi, ya sanya dokar hana fita ta sa’o’i 24 a garuruwan Yelwa-Tsakani, Yelwa-Lushi, Kagadama, da Birshi da ke bayan garin Bauchi tun daga yau Asabar.

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Malam Aminu Gamawa, shugaban ma’aikatan gidan gwamnatin jihar ta Bauchi ya fitar.

A cewarsa, matakin ya biyo bayan rikicin da ya ɓarke tsakanin al’ummar yankunan inda mutane uku suka rasa rayukansu, da dama suka jikkata, tare da ƙone wasu gidaje.

Ya ce an ɗauki matakin sanya dokar hana fita ne domin daƙile yunƙurin da wasu ɓata gari ke yi na hana zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin.

“Gwamnati ba za ta naɗe hannunta ta bar wasu masu aikata laifuka da masu mara musu baya su kawo cikas ga zaman lafiya da tsaron da ake samu a jihar Bauchi ba.

“Bayan wani taron gaggawa na tsaro da aka gudanar a yau, 28 ga Mayu 2022, an tura jami’an tsaro da dama domin dawo da zaman lafiya a yankunan da lamarin ya shafa.

“Ana bayar da kulawar jinya kyauta ga waɗanda suka jikkata kuma gwamnati ta bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike kan musabbabin tashin hankalin cikin ƙanƙanin lokaci.

“Saboda abubuwan da suka gabata, an sanya dokar hana fita ta sa’o’i 24 a Yelwa da kewaye, musamman a yankunan Lushi, Tsakani, Kagadama da Birshi na karamar hukumar Bauchi,” inji shi.

Ya ce matakin ba ya nufin kawo wa jama’a wahalhalu ba ne domin a dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali, inda ya ce za a sake duba lokutan dokar hana fita daga lokaci zuwa lokaci idan zaman lafiya ya dawo dai-dai.

Ya ƙara da cewa waɗanda aka samu da laifi za a hukunta su kamar yadda doka ta tanada, yana mai cewa jami’an tsaro sun kama wasu da ake zargi da hannu a lamarin.

Gamawa ya ce, an umarci Hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar Sema da ta gudanar da aikin tantance ɓarnar da aka yi tare da samar da kayayyakin agaji ga waɗanda lamarin ya shafa cikin gaggawa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here