Wata tankar mai ta fashe a ranar Alhamis a kan hanyar Legas zuwa Ibadan bayan ta yi karo da wasu motocin bas guda biyu.
Mista Ahmed Umar, Kwamandan hukumar kiyaye hadurra ta tarayya (FRSC) reshen Ogun, ya tabbatar wa manema labarai faruwar lamarin a Abeokuta.
“Babbam ne wanda ya hada da wata l tanka da wasu motoci biyu a kusa da wani wurin ibada da ke waje na babbar hanyar Legas zuwa Ibadan a ranar Alhamis.
“An shawarci masu ababen hawa da su yi taka-tsantsan kuma su natsu har sai an kashe gobarar,” in ji shi.
Umar ya tabbatar da cewa jami’an hukumar FRSC dana kashe gobara sun isa wajen da wuri domin tabbatar da zaman lafiya.













































