Wata wasika da shugaban kwamitin riko na jam’iyyar APC na kasa, Mai Mala Buni ya rubuta ta nuna cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari bai kore shi daga mukamin ba amma ya mika wa mai rikon kwarya kamar yadda ya kamata.
Solacebase ta ruwaito cewa wata wasika da Gwamna Mai Mala Buni ya rubuta, ta zargi Gwamna Nasir el-Rufai da yada labarin tsige shi a matsayin shugaban kwamitin tsare-tsare na musamman na rikon kwarya (CECPC).
Wasikar ta yi watsi da ikirarin El-Rufai na cewa an tsige Buni a matsayin shugaban jam’iyyar.
Lamarin dai ya kara dagula rikicin jam’iyyar APC.
Sansanin Buni ya yi ikirarin cewa Shugaban riko na APC ya mika al’amuran jam’iyyar ga Gwamna Abubakar Sani Bello a bisa doka kafin ya tafi neman lafiya kasar waje.
A cikin wasikar mai dauke da kwanan watan 28 ga watan Fabrairu, Buni ya umurci gwamna Bello da ya rike mukamin shugaban CECPC idan ba ya nan, domin zai yi tafiya zuwa kasar Dubai don jinya ba.
An aika kwafin wasikar hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) da daukacin mambobin CECPC.
Wasikar, wacce jaridar THE NATION ta samu, tana dauke da cewa: “Wannan shine don sanar da ku cewa zan fara ziyarar jinya zuwa Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) daga yau 28 ga Fabrairu, 2022.
“Ina mika muku ayyukan ofishina a matsayina na Shugaban Kwamitin Tsare-tsare na Musamman na Kasa (CECPC) zuwa gare ku.
“Wannan shi ne don baiwa kwamitin damar kammala duk shirye-shiryen da za su kai ga babban taron kasa da aka tsara a ranar 26 ga Maris, 2022 da sauran ayyukan da za a iya bukata daga ofishin.
A wata hira da gidan talabijin na Channels, el-Rufai ya ce samu sahalewar shugaban kungiyar gwamnonin APC, Gwamna Atiku Bagudu, wanda ya bayyana matakin da ya kai ga nadin gwamnan jihar Neja, Abubakar Sani Bello a matsayin mukaddashin shugaban jam’iyyar APC.
Wani mataimaki ga Buni, wanda ya nemi a sakaye sunansa, ya ce: “kungiyar gwamnoni ba zata iya tsige Buni ba, saboda wasikar sa ta fito fili. Ya bi tsarin da ya dace kuma ya zabi Bello ya yi masa aiki.
“Ya kamata gwamna el-Rufai ya gaya wa ‘yan Najeriya hakikanin abin da ya faru tsakanin shugaban kasa Muhammadu Buhari da wasu gwamnoni a ranar Lahadin da ta gabata. Bayanansa sun yi kuskure.
“Ya kamata ‘yan Najeriya su tambayi Bello da ‘yan CECPC ko irin wannan wasika ta zo musu daga Buni.”













































