Farashin iskar gas ɗin girki (LPG) ya ci gaba da tashin gwauron zabi a birnin Kano sakamakon ƙarancin samunsa a kasuwa.
Wasu daga cikin mazauna birnin, da suka yi magana da kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN, sun bayyana cewa wannan matsin farashin ya jefa su cikin ƙalubale wajen samun iskar gas ɗin girki.
Binciken da NAN ya gudanar a ranar Laraba ya nuna dogayen layuka a wuraren sayar da gas, yayin da wasu cibiyoyin na su ya ƙare gaba ɗaya.
Rahoton ya nuna cewa farashin ya ƙaru da kusan kashi 25 cikin ɗari cikin kwanaki biyar da suka gabata.
Ana sayar da kilo ɗaya na gas tsakanin Naira 1,800 zuwa Naira 2,000, yayin da cika kwalban kilo 12.5 ke kai tsakanin Naira 20,000 zuwa Naira 25,000 — sabanin tsohon farashin Naira 1,200 da Naira 14,000.
Wani dillali a unguwar Rijiyar Zaki, Sani Muhammad, ya bayyana cewa manyan wuraren ajiye gas kayan su ya ƙare, lamarin da ya haddasa ƙarancin samunsa a Kano.
Ya ce yawancin cibiyoyin gas ɗin sun rufe ko suna sayarwa a ƙananan adadi, wanda hakan ke ƙara wahalar da al’umma.
Ya danganta matsalar da takaddama tsakanin ƙungiyar direbobin manyan motoci masu ɗaukar kaya da kamfanin tace mai na Dangote, wanda ya shafi jigilar kayayyakin gas zuwa yankin.
Rahoton NAN ya ƙara da cewa wannan ƙarancin gas ya sa mutane da dama ke komawa amfani da gawayi da itace don dafa abinci, abin da ya haifar da yawaitar wuraren sayar da su a birnin Kano.
NAN












































