Ba Ganduje ko Gwamnatin Kano ke da hannun jari a tashar Tsandauri ta Dala ba – Hukumar Gudanarwa

Dala dry port

Hukumar gudanarwa ta tashar Tsandauri ta Dala (Dala Inland Dry Port) ta karyata rahotannin da ke cewa tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma tsohon Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ko iyalansa, suna da hannun jari a cikin kamfanin.

A cikin wata sanarwa da Sakataran Kamfanin, Barista Adamu Aliyu Sanda, ya fitar a ranar Laraba, hukumar ta bayyana rahotannin da ke yawo a kafafen sada zumunta da jaridu a matsayin ƙarya da ruɗani da kuma daidaita siyasa da ba ta da tushe.

Hukumar ta jaddada cewa babu ɗan gidan Ganduje ko Gwamnatin Jihar Kano da ke da wani kaso a cikin wannan shiri na tashar Dala.

Kamfanin ya bayyana cewa, binciken takardun rajista daga Hukumar Rijistar Kamfanoni ta Ƙasa (CAC) da kuma bayanan hukumomin kamfanin sun tabbatar da cewa babu wani daga cikin ‘yan gidan Ganduje da ya taɓa kasancewa mai hannun jari, darakta ko mai sa hannu a harkokin tashar Tsandauri ta Dala.

Hukumar ta bayyana cewa asalin mallakar tashar ya kasance a hannun wani ɗan kasuwa mai suna Ahmad Rabi’u, kafin Kamfanin City Green Enterprises (CGE) ya sayi kaso 80 cikin ɗari, ya bar Rabi’u da kaso 20 cikin ɗari.

An kuma gudanar da wannan ciniki cikin doka da bayanai a CAC, ba tare da wani hannun Gwamnatin Jihar Kano ko gidan Ganduje ba.

Labari mai alaƙa: Hukumar yaƙi da cin hanci ta Kano ta fara bincike kan Naira biliyan 4 da ake zargin an karkatar a zamanin Ganduje zuwa tashar Tsandauri ta Dala

Dangane da rahotannin da ke cewa an bai wa ‘ya’yan Ganduje hannun jari miliyan biyar-biyar hukumar ta ce takardar da ake nunawa ƙirƙira ce da aka yi domin haifar da rikici, kuma ba tare da sanin sauran daraktoci ba.

Hukumar ta ƙara da cewa, batun cewa Gwamnatin Jihar Kano na da kaso 20 cikin ɗari a kamfanin ma ƙarya ce.

Ta bayyana cewa haɗin gwiwar jihar kawai ya ta’allaka ne da taimakon ci gaban al’umma (CSR) da aka bayar a lokacin da Hukumar Kula da Jiragen Ruwa ta Najeriya (NSC) ta roƙi taimako wajen gyaran wurin Zawaciki domin farfaɗo da ayyukan tashar.

Hukumar ta kuma karyata rahoton da ke cewa wani jami’in gwamnatin Kano mai suna Abdullahi Haruna yana wakiltar jihar a kwamitin gudanarwa, tana mai cewa ba mu taɓa sanin ko yin hulɗa da wannan suna ba a tarihin kamfanin.

Kamfanin ya bayyana cewa, yaɗa waɗannan labaran ƙarya wani yunkuri ne na wasu masu son rikici domin bata sunan Dakta Ganduje da kuma rage amincewa da ci gaban da ake yi a aikin tashar.

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here