Amurka ta amince ta mayar da karin dala miliyan 23 ga Najeriya.
Kudaden dai wani bangare na kudaden da ake zargi tsohon shugaban mulkin sojan kasar Sani Abacha ya sata.
A ranar Talatar da ta wuce ne kasashen biyu suka cimma yarjejeniya a Abuja kan batun kudin.
Ministan Shari’a na Najeriya, Abubakar Malami, ne ya sanya hannu a yarjejeniya, yayin da jakadar Amurka a kasar Maru Leonard, ta wakilci kasarta a yarjejeniyar.
Malami ya ce idan an dawo da kudin za a kashe su ne wajen ayyukan gina kasa.
A 2020, Amurka ta dawo wa Najeriya da fiye da dala miliyan 300.
Ana zargin tsohon shugaban kasar Abacha, da ya rasu a 1998, da sace biliyoyin dalolin kasar tare da ajiye su a kasashen waje.
Kazalika a shekarun baya-bayan nan gwamnatin Najeriya ta dawo da wasu kudaden da aka sace aka boye su a kasashe kamar Switzerland da Burtaniya da kuma Amurka.













































