Gwamnatin Kano da bakin dunyi zasu gina tituna masu tsayin kilomita 6,300 a duk kauyikan da ke jihar.
Shugaban hukumar da ke kula da kauyuka da harkokin noma (RAAMP), Yahaya Adamu Garin Ali, ne ya sanar da hakan a ya yin wani taron bada horo na kwana biyu kan dabarun da za’abi wajan kididiga da bada bayanai na hanyoyi da tititunan da ke kauyikan jihar.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar, Adamu Abdullahi, ya fitar ranar Talata, yace Garin Ali ya bayyana kokarin da gwamnatin jihar take wajan ganin an samar da hanyoyi da kuma habbaka harkar noma da kiwo a fadin jihar baki daya.
‘”Sanan kuma shugaban hukumar ya ja hankalin wadanda aka bawa horon dasu bada himma da sadaukarwa wajan ciyar da mutanan jihar kano gaba.” Inji sanarwar.













































