Bayan samun lafiya da yayi, mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo a yau Talata ya halarci taron Majalisar Zartaswa ta Tarayya FEC, wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ke jagoran ta a fadarsa da ke Abuja.
An yiwa Osinbajo aiki ranar 16 ga watan Yuli na shekarar 2022, a asibitin Duchess International Hospital, da ke Ikeja a cikin jihar Lagos.
Bayan ansami nasarar yi masa aikin an salame daga asibitin a ranar 25 ga watan Yuli.
Mataimakin shugaban kasan ya nuna firincikin sa da godiya ga ‘yan Najeriya bisa fatan alkairi da kuma addua’ar da su kai masa yayin aikin.