Gwamna Babagana Zulum na jihar Barno ya bada Naira miliyan biyar ga wata makaranta mai zaman kanta domin daukar nauyin karatun Musa Sani, yaro dan shekara 13 mai hazaka a Barno wanda yai amfani da laka ya kwaikwayi ginin gadar sama ta farko a jihar.

gwamnan ya biya kudin ne ga makarantar Golden Oliver Academy, Maiduguri domin daukar nauyin karatun Musa daga Firamare har kammala babbar sakandare.

A dai cikin kwanakin nan ne hankalin Zulum ya kai kan Musa bayan ya yi amfani da laka ya gina gadar sama da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar a watan Disamba a cikin garin Maiduguri, Zulum ya yi sha’awar basirar da yaron keda ita, hakan yasa gwamnan ya nemi ganin iyayen yaron kuma ya bada tallafin karatun don inganta bisirar sa














































