Kungiyar Mata Manoma ta WOFAN-ICON 2 ta bukaci kafa shirye-shiryen karfafa gwiwa don taimakawa wajen rage talauci da samar da zaman lafiya a tsakanin al’umma.
Dakta Salamatu Garba, Daraktar kungiyar ta WOFAN-ICON 2 ce ta bayyana hakan yayin wani taro da aka gudanar a birnin Landan ranar Laraba.
Jaridar SolaceBase ta rawaito cewa taron wani bangare ne na ayyukan bikin Ranar Zaman Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya.
Salamtu ta jaddada cewa samar da kungiyoyi ko wuraren zama, inda ake tallafawa masu cin gajiyar a kungiyance, na iya yin tasiri sosai.
Ta bayyana cewa, wannan tsarin ba wai yana taimakawa wajen rage radadin talauci ba, har ma da samar da zaman lafiya ta hanyar shiga tsakanin mutane da rage rikice-rikice.
Wadanda suka halarci wannan horon sun hada da masu tsara manufofi, malamai, ‘yan siyasa, shugabannin gargajiya, da ‘yan jarida.
An shirya wannan horaswar ne tare da goyon bayan gidauniyar MasterCard, kuma ta mai da hankali kan hada manoma da masu sarrafa amfanin gona don juya noma zuwa kasuwancin da zai riba.
Masaniyar da ta jagoranci taron, Vidjea Galkwad, ta tattauna kan batutuwa kamar ilimin hali, tsarin shugabanci, dabarun sadarwa, da kuma gina haɗin kai da amana a cikin ƙungiyoyi.