An dakile yunkurin juyin mulki a jamhuriyar Benin, an kama kwamanda da tsohon minista

File photo of Benin soldiers 750x430

Hukumomin Jamhuriyar Benin sun hana wani yunkurin juyin mulki, inda aka kama tsohon ministan wasanni da babban kwamandan soja.

Ana zargin cewa shirin zai faru a ranar Juma’a mai zuwa, kamar yadda Elonm Metonou, mai gabatar da kara na musamman a kotun laifukan kudi da ta ta’addanci ta Benin, ya bayyana.

A daren Talata, an kama Oswald Homeky, tsohon ministan wasanni, yana mika jakunkuna guda shida na kudi, jimillar su CFA biliyan 1.5 na Yammacin Afirka (kimanin dala miliyan 2.5), ga Djimon Dieudonne Tevoedjre, kwamandan rundunar gadi na shugaban kasa, kuma shugaban tsaron Shugaba Patrice Talon.

An kama shi da misalin karfe 1:00 na safiyar Talata yayin mika kudin, kuma an bayyana cewa an yi amfani da motar Toyota Prado mai faranti na bogi wajen safarar kudin.

Masu gabatar da kara sun bayyana cewa kudin na daga cikin wani makarkashiya da Homeky da Olivier Boko suka shirya, wanda shi ne abokin shugaba Talon na dogon lokaci kuma hamshakin dan kasuwa.

Boko, wanda aka kama daban a ranar Litinin a Cotonou, ya bayyana kudurinsa na tsayawa takarar shugaban kasa a shekarar 2026, lokacin da wa’adin shugaba Talon zai kare.

Bincike ya nuna cewa Homeky da Boko sun biya kwamandan sojan ne domin kada ya yi jayayya da yunkurin juyin mulki.

Hukumomi sun kuma gano cewa wadanda ake zargi sun bude asusun banki a Côte d’Ivoire da sunan kwamandan tun ranar 6 ga watan Agusta, a wani bangare na shirinsu.

Kamen ya zo ne a daidai lokacin da ake yawan sukar gwamnatin shugaba Talon, inda masu suka ke zarginsa da rage karfin dimokuradiyya.

Hukumomi suna ci gaba da bincike domin kama sauran wadanda ke da hannu cikin wannan makarkashiya.

Tun daga shekarar 2020, kasashen Yammacin Afirka sun sha fama da juyin mulki da yunkurin hakan, kuma yanzu haka Benin ta shiga jerin kasashen da ke fuskantar barazana ga zaman lafiyar siyasa.

Metonou ya tabbatar da cewa ana kokarin ganin an yi adalci tare da hana duk wani yunkuri na lalata kasar nan gaba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here