Babbar jam’iyyar adawa a Nigeria PDP ta bayyana cewa ta tsaf domin sake gina Nigeria ta hanyar dawo da hadin kai da kaunar juna tare da tabbatar da bin doka da oda tsakanin al’ummar kasar.
Shugaban jam’iyyar na kasa Sanata Iyorchia Ayu ne ya bayyana hakan a wajen wata liyafar taya shi murna da aka yi a gidan gwamnatin jihar Benue.
Ya ce gwamnatin Shugaban kasa Muhammdu Buhari ta raba kan ‘yan kasa tare da kirkiro da talauci, wanda hakan ya janyo rashin aminci tare da assasa kabilanci da rigingimu da suka shafi addini.
Ya kara da cewa har yanzu cewa har yanzu gwamnatin APC ta kasa cika alkawuran da ta dauka lokacin zabe, inda ta mayar da hankali wajen kirkirar karya domin kawar da hankalin ‘yan Nigeria Saboda gudun kada ayi musu bore.
Sanata Ayu ya ce yanzu haka jam’iyyar PDP tana aiki ba dare ba rana domin fito da tsare-tsaren da za su gyara kasar, idan sun karbi mulki a shekarar 2023.
Ya kuma yi kira ga ‘yan Nigeria kada su cire tsammani kan gyaruwar kasan nan, yana mai cewa don APC ta Nigeria hakan baya nufin PDP ba zata iya gyara ta ba, inda yace tuni suka gama shirin samar da shugabanci na gari wanda zai kare rayuwa da dukiyar ‘yan kasa tare da korar fatara da talauci ta hanyar bunkasa tattalin arziki tare da samarwa matasa aikin yi.












































