Kaduna: Gwamna ya bada umarnin gudanar da bincike kan harin da sojoji suka kai wani kauye a Jihar

Tudun Biri attack 720x430
Tudun Biri attack 720x430

Gwamnan Kaduna Uba Sani, ya bukaci jama’a da su kwantar da hankali kan samamen da sojoji suka kai wanda ya yi sanadiyar rasa rayukan sama da mutane 50 a yayin bikin Mauludin da aka yi a karamar hukumar Igabi ta jihar.

A cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun sakataren yada labaransa Muhammad Lawan Shehu, Uba Sani ya kuma bada umarnin gudanar da bincike kan lamarin.

Rundunar sojin Najeriya ta dauki alhakin faruwar lamarin inda ta bayyana cewa jami’anta na gudanar da wani aiki ne domin yakar ‘yan ta’adda amma ba da gangan suka afkawa al’ummar ba.

Yace gwamnatinsa ta tsaya tsayin daka don hana sake afkuwar wannan ibtila’i tare da tabbatar wa mazauna Kaduna cewa za a ba da fifikon kare su a ci gaba da yaki da ‘yan ta’adda da sauran miyagun laifuka.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here