Gidan Mundubawa na tsohon gwamnan jihar Kano Mallam Ibrahim Shekarau ya kone kurmus, inda ta lalata dakunan matarsa ta uku, Halima Shekarau.
SolaceBase ta raiwato cewa gobarar da ake zargin ta taso ne daga kicin na gidan, a daren Lahadi ba a iya gano musabbabin tashin gobarar ba.
Karin labari: Dan Jarida ya sha da kyar bayan harbinsa da harsashi a gidan gwamnatin Kano
Da yake tabbatar da faruwar lamarin ga SolaceBase, mai baiwa Malam Ibrahim Shekarau shawara kan harkokin yada labarai, tsohon Sanatan Kano ta tsakiya kuma tsohon ministan ilimi, Dokta Sule Ya’u Sule, ya ce gobarar ta tashi ne da yammacin ranar daga dakin girki na cikin gidan da ke a kasa wanda aka kashe miliyoyin nairori.
Ya ce, “Mun gode wa Allah da gobarar ta shafi daya daga cikin dakin Malam Ibrahim Shekarau ne kawai, kuma tuni jami’an hukumar kashe gobara ta jihar suka yi nasarar kashe gobarar.
Karin labari: Hajjin 2024: NAHCON ta sanar da ranar fara jigilar maniyyata zuwa kasar Saudiyya
Kakakin Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Saminu Yusuf Abdullahi da aka tuntube shi ya tabbatar da faruwar lamarin, sai dai ya bayyana cewa ba zai ce uffan ba kan musabbabin tashin gobarar amma suna ci gaba da daidaita al’amura.