Dan Jarida ya sha da kyar bayan harbinsa da harsashi a gidan gwamnatin Kano

Gidan, Gwamnatin, Kano, dan jarida, harbi
Wani Dan Jarida Naziru Idris Ya’u da ke aiki a gidan talabijin na Abubakar Rimi, ARTV ya sha da kyar tun bayan harbinsa da harsashi a gidan gwamnatin jihar...

Wani Dan Jarida Naziru Idris Ya’u da ke aiki a gidan talabijin na Abubakar Rimi, ARTV ya sha da kyar tun bayan harbinsa da harsashi a gidan gwamnatin jihar Kano.

SolaceBase ta rawaito cewa tushen harsashin da har yanzu ba a san shi ba ya afkawa wakilin a cikin gidan gwamnati da misalin karfe 6:30 na yammacin ranar Juma’a.

Lamarin ya faru ne a daidai lokacin da ake gudanar da bikin ranar ‘yancin ‘yan jarida ta duniya da Majalisar Dinkin Duniya ta ware, a ranar 3 ga watan Mayun kowacce shekara.

Karin labari: Hajjin 2024: NAHCON ta sanar da ranar fara jigilar maniyyata zuwa kasar Saudiyya

Nazir Ya’u wanda a nan take aka garzaya da shi asibitin gidan gwamnati ya ce har yanzu ba a san asalin harsashin da ya yi ba.

An sallami dan jaridar da ya samu rauni daga baya, bayan an yi masa magani.

Wani ma’aikacin lafiya a asibitin ya ce dan jaridar ya yi sa’a saboda harsashin da aka harba ba a kusa ba.

Karin labari: Kano: Karnuka sun cinye sassan jikin jaririya sabuwar haihuwa da aka jefar a unguwar Gaida

Bayan afkuwar lamarin, jami’an ‘yan sanda da ke gidan gwamnati sun fara gudanar da cikakken bincike don gano musabbabin faruwar lamarin.

Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, babu wata sanarwa a hukumance daga fadar gwamnatin Kano dangane da harbin.

Karin labari: Kungiyar kwadago ta NLC a Kano ta koka da koma bayan fansho da ba a biya

Sai dai shirun da aka yi a kan lamarin ya haifar da ce-ce-ku-ce da rashin kwanciyar hankali a tsakanin ‘yan jarida, lamarin da ke nuna irin hadarin da ‘yan jarida ke fuskanta hatta a wuraren da ake zaton na tsaro ne.

SolaceBase ta tuntubi Kakakin Gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa a ranar Asabar amma layin wayarsa bai shiga ba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here