A Guri Guda ‘Yan Aji 1,2,3 Ke Daukan Darussa, Haka Ma ‘Yan Aji 4,5,6 Awata Makaranta Anan Kano.

F 1
Al’ummar Garin Faradaci a karamar hukumar Sumaila a jihar Kano, ba su da kowace irin ababen more rayuwa ta al’umma tun daga kyawawan hanyoyi da kiwon lafiya…

A wani binciken kwakwaf da Jarida Solacebase tayi ta gano cewa Al’ummar yankin Faradaci da ke karamar hukumar Sumaila a Jihar Kano, ba su da kowacce irin waayewa da kayan ababen more rayuwa tun daga kyawawan hanyoyi, kiwon lafiya, makarantu da sauran su wadanda za su inganta yanayin rayuwa.

Al’ummar yankin dake kudancin Kano sun kwashe kusan shekaru takwas suna fama da rubabbiyar makarantar firamare mai dalibai sama da 500.

Makarantar tana da tazarar nisan kilomita 75 daga birnin Kano, Makarantar firamare dake Faradaci ita ce ke zama cibiyar ilimi daya tilo a garin a tsawon shekaru da dama.

A cewar mazauna yankin, a lokacin damina ana hada yara dalibai ‘yan firamare na aji 1, 2 da 3 zuwa aji guda domin daukar darasi yayin da na azuzuwan 4,5 da 6 suke tattaruwa a wani aji guda domin karbar darussa sakamakon halin da makarantar ke ciki na rashin rufin dakunan ajin.

Kayayyakin makarantar na cikin mawuyacin hali, inda ajujuwa da dama ba su da rufin kwano, lamarin da ke sa ake rika rufe makarantu a lokutan damina.

“Makarantar ta kasance batada ingantaccen rufin na tsawon shekaru bakwai zuwa takwas,” Suraj Muhammad Idris, wani malami a makarantar ya shaida wa jaridar SolaceBase.

“Lokacin da aka yi ruwan sama, ba mu da wani zabi illa mu rufe makarantar ko kuma mu hada ajujuwa uku zuwa hudu wuri daya, wanda hakan ke kawo cikas ga harkar koyo.”

Mazauna garin sun shaida wa SolaceBase cewa sun dade suna bayyana damuwarsu game da tabarbarewar makarantar firamare daya tilo da ke garin kuma duk da korafe-korafe da kuma alkawurran shiga tsakani da aka yi, lamarin ya gagari kundila.

Wani malami a makarantar Sulaiman Muhammad ya ce rashin isasshen ajujuwa na daya daga cikin matsalolin da makarantar ke fuskanta.

“Tare dacewa dalibai sama da 500 ne a makarantar tana cike da cunkoson jama’a, wanda ya sa ya zama aiki mai wahala wajen samar da ingantaccen ilimi.”

“Rashin kayan koyo ya kara dagula al’amura, wanda hakan ya sa dalibai da malamai ke fafutukar ganin sun ci gaba da bin tsarin karatun.”

“Wani abin da ya kara dagula makarantar shi ne kasancewar filin da aka gina makarantar ma ba na makarantar firamaren ba ce, makarantar Islamiyya ce,” inji Muhammad.

Armaya’u Musa, yana da ‘ya’ya biyu da ke halartar makarantar, ya nuna rashin jin dadinsa da rashin daukar mataki daga gwamnati keyi duk da kiran da suke yi na akawo musu dauki.

“Ya’yanmu sun cancanci fiye da wannan.”

Shugaban al’ummar garin Faradaci Malam Jazuli Kabiru Idris ya koka kan halin da makarantar firamare daya tilo a cikin al’umma ke ciki.

Dangane da wannan korafin, Umar Haruna Doguwa, Kwamishinan Ilimi na Jihar Kano ya amince dacewa tabbas akwai wannan matsalar ga SolaceBase, inda ya dora alhakin yanayin makarantar a kan gwamnatin da ta gabata.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here