Rundunar yan sanda reshen jihar Kaduna ta ce jami’anta sun samu nasarar kashe kasurgumin ɗan bindigan jeji, wanda ya addabi mutane a jihar. Bayan halaka ɗan ta’addan, dakarun ‘yan sanda sun kwato Babur ɗin da suke amfani da shi a ƙauyen Kidandan, ƙaramar hukumar Giwa, a Kaduna.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan, DSP Mohammed Jalige, ne ya tabbatar da haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi a Kaduna.
Jalige ya ce: “Ranar (Lahadi) 7 ga watan Mayu, 2023 da misalin karfe 10:30 na safe, dakarun yan sandan da suka fita sintiri a kan Titin Fatika, suka ci karo da tawagar yan bindiga a kan Babura, sun yi shigar Sojoji.”
“Nan take gwarazan jami’an yan sanda suka tarbe su, aka yi musayar wuta kuma sun nuna wa yan bindigan ruwa ba sa’an kwando bane. Sun sheƙe ɗaya daga cikin yan bindigan wanda ya sanya kakin soji.”
“Sauran yan bindigan suka ari na kare ɗauke da muggan raunukan harsashin bindiga, haka nan jami’an sun kwato Babur ɗin da maharan ke amfani da shi.”
A cewarsa, jami’an yan sanda ba su kwanta ba, sun kara tsananta sintiri a kan Titin domin dakile duk wani hari da yan ta’addan ka iya ƙara yunkurin kaiwa.
Jalige ya ƙara da cewa kwamishinan ‘yan sanda a Kaduna, Musa Garba, ya jinjinawa kwazon da dakarun suka nuna wanda ya basu wannan nasara. Ya ce kwamishinan ya roki jami’an kar su gajiya su ɗora daga nan kan yan bindigan jeji da sauran muggan laifuka a jihar Kaduna.













































