Shugaban jami’ar, Farfesa Abdul-Rashaeed Na-Allah ya ce jami’ar tana daukar tsau-tsauran mata kai akan malaman nata dake neman dalibai, inda ya kara da cewa jami’ar a baya ta kuri shehinan malaman jami’ar har guda biyu akan irrin wananan laifen na amfani da dalibai mata kafin a basu maki su ci jarrabawa.
Na’Allah ya shaidawa kamfanin dillan cin labarai na Najeriya NAN cewa jami’ar tuni ta kaddamar da dokoki da suka hana neman dalibai a cikin jami’ar baki daya.
Shugaban jami’ar wanda yanzu haka yana kasar Amerika domin haduwa da tsofafin daliban jam’ar, ya ce dalibai mata suna da bukatar a basu kariya ta kowa ce fuska.
Ya kara dacewa: “ abin takai ci ne kaga malaman da sune yakamata ace suna bawa daliban kariya daka dukkan matsaloli kuma yanzu sune suka zamo matsalar ta su.
“ duk da cewa wannan matsalar ta shafi jami’o’in najeriya ba wai iya jami’ar mu ce kadai ke fuskantar matsalar ba.
“yanzu haka akwai kwamatin da jami’ar ta kafa don yin binkice akan matsalar domin magan ce ta, yin hakan na daya daga cikin matsalolin da jami’ar zata magan ce ta shiga sahun zakakoran jami’o’in najeriya.
inda Ya kara da cewa jami’ar tana kokari wajan habbaka kayan aiki ga dalibai, wadan da suka hada da na’urori na zamani a cikin jami’ar baki daya.













































