Hukumar shirya jarabawar shiga manyan makarantun gaba da sakandire ta JAMB ta bada tabbacin cewa babu wani dalibi da zai eubuta jarrabawar a wata cibiyar da ba a ban ya yi rajista ba.
Dakta Fabian Benjamin, mai ba da shawara da kuma hulda da jama’a na hukumar JAMB, ya ba da wannan tabbacin a wata tattaunawa ta wayar tarho da kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) a ranar Talata a Abuja.
Benjamin ya bayyana cewa, wasu daliban suka rubuta jarrabawar (UTME) ta 2025 an tura su wajen jiharsu, amma sai suka samu damar yin jarrabawar a yankunan su.
Karanta: Jami’o’in Najeriya da dama na karrama marasa ilimi, wadanda ba su cancanta ba – Jega
A cewarsa, hakan ba zai sake faruwa ba a babbar jarrabawar domin za a samu karin cibiyoyi da za su gudanar da jarrabawar don haka ba za a tura kowanne dalibi wajen jiharsa ba.
A wata sanarwa da Benjamin ya fitar a ranar Lahadin da ta gabata ya ce hukumar ta amince da jinkiri da sauran kalubalen da wasu daliban suka samu a lokacin jarrabawar kuma ta yi nadamar duk wata matsala da aka samu.
An shirya fara jarabawar UTME ta 2025 a ranar 25 ga Afrilu. (NAN)