Shugaban Jami’ar Bayero da ke Kano (BUK), Farfesa Sagir Adamu Abbas, ya tabbatar da nadin gogaggen dan jarida Lamara Garba a matsayin babban darakta na sashin hulda da jama’a.
A cewar wata sanarwa ta musamman da aka fitar a ranar Alhamis, ta ce nadin wani gagarumin ci gaba ne da ke nuna kokarin da jami’ar Bayero Kano ke yi na karfafa tsarin gudanarwa da sadarwa.
SolaceBase ta ruwaito cewa an tabbatar da nadin ne a wata takarda a hukumance mai dauke da sa hannun magatakardar Jami’ar, Malam Haruna Aliyu, a ranar 22 ga Afrilu, 2025.
Sanarwar ta ce Lamara Garba ya kasance mataimakin magatakarda mai kula da hukumar tun a shekarar 2021. Ana kallon wannan nadin a matsayin ci gaba mai ma’ana da kuma samun ci gaba mai kyau, la’akari da dimbin gogewarsa da sadaukarwar da yake da shi ga aikin gwamnati.
“Kwararren masanin aikin jarida, sadarwar jama’a, da gudanar da mulki, Lamara Garba ya kai fiye da shekaru 30 ds kwarewa a kan dabarun aiki a matsayin da yake,” in ji sanarwari.
Lamara wanda aka haife shi a watan Disamba 1966 a garin Azare da ke karamar hukumar Katagum a jihar Bauchi, ya fara samun kwarewa a shekarar 1993 a matsayin wakilin New Nigerian, inda yake bayar da rahotannin manyan al’amura da abubuwan da suka faru a fadin jihohin Kaduna, Bauchi, Kano, da Jigawa.
Salon bayar da rahotonsa, wanda ya samo asali ne cikin daidaito da kwarewa, ya sa aka girmama shi a harkar yada labarai. Ya rike mukamin Shugaban Kungiyar ‘Yan Jarida ta Jihar Kano na tsawon wa’adi biyu. Daga nan ya rike muhimman mukamai a matakin kasa, ciki har da Shugaban Sadarwar Dabaru a Hukumar Kula da Kudi a Fadar Shugaban ƙasa da ke Abuja, da shugaban sashen yada Labarai na hukumar Jarabawa ta Kasa (NECO) da ke Minna.
A shekarar 2015, Malam Garba ya shiga hidimar jami’ar Bayero ta Kano, inda ya taka rawar gani wajen karfafa sadarwa ta jami’o’i, da tallafa wa ayyukan ci gaban jami’o’i, da kuma wayar da kan jama’a.
Ya kammala karatunsa na BUK, ya yi digirin digirgir na B.A. da M.Sc. a sashin sadarwa. A yanzu haka yana karatun PhD) a dai sashin sadarwa jami’ar.
A matsayinsa na Daraktan Hulda da Jama’a, aikinsa zai hada da kula da dabarun sadarwar jama’a a jami’ar, da kula da huldar yada labarai, da kuma daidaita kokarin wayar da kan jama’a.
Shugaban jami’ar ya kara da cewa ana sa ran shugabancinsa zai kawo sabon salo kan yadda jami’ar ke tafiyar da kanta ga jama’a da kuma mu’amala da masu ruwa da tsaki.
Lamara Garba msmba ne na kwararrun kungiyoyi da suka hada da kungiyar ‘yan jarida ta Najeriya (NUJ), Cibiyar kwararru kan hulda da Jama’a ta Najeriya (NIPR), Kungiyar hulda da Jama’a ta Afrika (APRA), Kungiyar Malaman Sadarwa da Masana Sadarwa ta Najeriya (ACSPN), da ACCE da dai sauransu.
Tare da nadin Malam Garba, Hukumar ta kuma sanar da wasu sabbin mukamai na shugabanci a sashin Rajistara da Bursary.
Wadanda naɗin ya shafa sun hada da Hajiya Halima Shehu Hayatu, wacce aka nada a matsayin babbar Darakta a hukumar gudanarwa ta kasa, wacce ke da alhakin gudanar da ayyukan ci gaba, sai Hajiya Altine Maryam Ali, wacce aka tabbatar da ita a matsayin Babbar Darakta, ta kawo kwakkwarar tushe a tsarin gudanarwa da aiwatar da manufofi.
Hajiya Anisatu Uwaisu Muhammad an nada ts Darakta, wanda aka yi mata kallon yadda take gudanar da ayyukanta da kuma mai da hankali kan jin dadin ma’aikata da inganta ayyukanta.
Hakazalika, Dskta Garba Abdullahi Barume, wanda aka nada shi Darakta, ya kawo kwarewar ilimi da kuma jagoranci mai zurfin tunani.
A cikin Sashen Bursary, an nada ƙwararru guda biyu don haɓaka sa ido kan kuɗi da lissafi:
Malam Rabiu Ibrahim Maitafsiri, wanda aka nada shi Darakta na Ƙididdiga da Rahoto/kssafi, wanda ke da alhakin sarrafa rahotannin kuɗi da tallafawa ayyukan kasafin kuɗi, sai Usman Gomina Ohikere, shi ne aka nada Daraktan Kuɗi mai kula da samar da kuɗin shiga da kuma kula da tsare-tsaren kuɗi.
Wadannan nade naɗen suna nuna ƙoƙarin haɗin gwiwar jami’a don haɓaka tasirin gudanarwa ta hanyar shigar da ƙwararru tare da ingantaccen aiki da jagoranci. Ana sa ran mutanen da aka zaɓa za su yi aiki tare don inganta ayyukan cikin gida, da tallafawa manufofin jami’a na dogon lokaci.