Jami’ar Maryam Abacha dake Kano ta nada shugaban jami’ar tarayya dake Dutsinma (FUDMA) Farfesa Armaya’u Bichi a matsayin mamba a majalisar gudanarwarta.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na jami’ar ta FUDMA, Malam Habib Umar-Aminu ya fitar ranar Asabar a Katsina.
Ya bayyana cewa nadin na Farfesa Bichi ya biyo bayan taron kwamitin amintattu na jami’ar ta Maryam Abacha, wanda aka gudanar a ranar 15 ga watan Fabrairu.

Da yake taya wanda aka nada murna shugaba kuma wanda ya kafa jami’ar ta MAAUN, Farfesa Adamu Gwarzo, ya ce zabin nasa ya biyo bayan binciken kwakwaf da aka yi a tsakanin fitattun mutane domin hazaka da jajircewarsu wajen bunkasa ilimi da ci gaban al’umma.













































