Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara a ranar Asabar ta tsare Malam Umaru Maradun, wakilin Jaridan Leadership, bisa wani dalili da ba a bayyana ba.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Ayuba Elkanah, ya kuma tabbatar da kama shugaban kungiyar ‘yan jarida ta Kasa reshen jihar, Ibrahim Maizare.

Yanzu haka dai Maradun yana tsare a sashin binciken manyan laifuka (CID) inda shugabannin kungiyar NUJ suka nemi belin sa amma ‘yan sanda suka ki amincewa.












































