BIDIYO: ‘Yan Ta’adda Sun yi wa mutanen da aka sace a Jirgin Kasan Abuja zuwa Kaduna Bulala

Bandits
Bandits

Wani sabon faifan bidiyo da ke yawo a kafar Internet ya nuna yadda ‘yan ta’adda ke dukan wadanda aka sace a jirgin kasa dake kan hanyar Abuja zuwa Kaduna tun a ranar 28 ga watan Maris na shekarar 2022.

Faifan bidiyon ya nuna yadda ‘yan ta’addan ke yi wa wadanda suka sace bulala ba ji ba gani ba bayan da suka yi barazanar kashe sauran mutane 43 da suka rage a hannunsu.

A cikin faifan bidiyon, daya daga cikin ‘yan ta’addan ya ce matukar gwamnati ba ta biya musu bukatunsu ba, to kuwa zasu ci gaba da cin karensu babu babbaka.

“Wannan shi ne sakonmu ga gwamnatin Najeriya kuma kamar yadda kuka ga wadannan mutane a nan, da yardar Allah za ku ga shugabanninku; Sanatoci da gwamnoninku za su zo gabanmu.

“Wadannan da kuke gani a nan za mu ajiye wasu a matsayin bayi mu sayar da su kamar yadda shugabanmu ya fada muku a baya,” inji shi.
Jaridar Solacebase ta Turanci ta cika shekaru biyar

Wannan na zuwa ne makonni kadan bayan harin da aka kaiwa ayarin motocin shugaban kasa Muhammadu Buhari a jihar Katsina a lokacin da tawagar shugaban kasar ke kan hanyarsu ta zuwa Daura.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here