PSC / FCCPC: Shugaba Tinubu ya aike da sunayen mutane 3 ga Majalisar Dattawa

PSC, FCCPC, Shugaba, Tinubu, aike, sunayen, mutane, Majalisar, Dattawa
Shugaba Tinubu ya mika sunayen mutane uku da aka nada domin tantancewa da tabbatar da nadinsu a matsayin shugaba da sakatare da kuma memba na Hukumar...

Shugaba Tinubu ya mika sunayen mutane uku da aka nada domin tantancewa da tabbatar da nadinsu a matsayin shugaba da sakatare da kuma memba na Hukumar Sabis ta ‘Yan Sanda (PSC).

An mika sunayen ne ga Majalisar Dattawan Najeriya a yayin da ake ci gaba da wani sabon zaman majalisar a ranar Alhamis.

Wadanda aka nada sune:

Mataimakin Sufeto Janar na ‘yan sanda (DIG), Hashim Argungu a matsayin (Shugaba), sai kuma Cif Onyema Uche a matsayin (Sakataren), da kuma DIG Taiwo Lakanu a matsayin (memba) mai ritaya na PSC.

Karin labari: “Za’a cimma matsayar tattaunawar mafi karancin albashi” – Cewar Gwamnonin Najeriya

Tinubu ya kori Sufeto Janar na ‘yan sandan Najeriya Solomon Arase mai ritaya a matsayin shugaban hukumar a farkon watan nan.

Wannan dai na zuwa ne yayin da hukumar ta PSC ke fafatawa da Sufeto-Janar na rundunar ‘yan sandan Najeriya, Kayode Egbetokun kan abin da ta kira katsalandan wajen daukar ‘yan sanda aiki.

Wannan ya sa PSC, ta yi kira ga Tinubu, ya sallami Egbetokun.

Karin labari: VC: An zabi Farfesa Aisha Maikudi a matsayin mukaddashin shugaban jami’a

Shugaba Tinubu ya kuma bukaci majalisar dattijai da ta duba tare da tabbatar da nadin Dakta Olatunji Bello domin nada shi a matsayin babban jami’in gudanarwa na mataimakin shugaban hukumar FCCPC.

An mika sunan Bello ga kwamitin kasuwanci da saka hannun jari na Majalisar Dattawa, yayin da na Argungu, Uche da Lankano aka mika shi ga kwamitin majalisar dattijai mai kula da harkokin ‘yan sanda don ci gaba da gudanar da ayyukan majalisa, don gabatar da rahoto nan da mako guda.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here