Rundunar ‘yan sandan jihar Benuwe ta cafke biyu daga cikin ‘yan fashi da makami da suka kai hari ofishin ‘yan sanda tare da kashe jami’ai a Otukpo da ke jihar Benue a ranar Juma’a.
‘Yan fashin kafin su kai hari ofishin ‘yan sanda sun kai samame a wasu bankuna da suka hada da First Bank, United Bank for Africa, Zenith Bank, Access, da Stanbic Bank, kuma sun yi awon gaba da wasu kudade da ba a tantance adadinsu ba.
A wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Benuwe, Catherine Anene ta fitar a ranar Asabar, ta bayyana cewa jami’an tsaro sun cafke ‘yan fashin a kan hanyar Otukpo-Taraku inda suka kashe biyu daga cikinsu.












































