Hambararren Shugaban Kasar Nijar Yayi Kokarin Tserewa – Sojoji 

Mohammed Bazoum Niger Republic
Mohammed Bazoum Niger Republic

A ranar 20 ga Oktoba, 2023 Mohammed Bazoum, Tsohon Shugaban Jamhuriyar Nijar yayi kokarin tserewa daga hannun sojojin dake tsare dashi.

Sai dai sojojin Nijar din  sun ce sun dakile yunkurin Mohamed Bazoum, tsohon shugaban kasar da suka hambarar a juyin mulki a watan Yuli, daga tserewa daga hannunsu a ranar Alhamis.

“Da misalin karfe uku na safe, hambararren shugaban kasar Mohamed Bazoum da iyalansa, masu dafa masa abinci biyu da jami’an tsaro biyu, sun yi kokarin tserewa daga inda ake tsare da shi,” in ji kakakin gwamnatin Amadou Abdramane a gidan talabijin na kasar.

Yukurin tserewa ya ci tura kuma an kama wadan da suke da hannu wajen bashi gudun mawar tserewa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here