Magaji Garin Zazzau, Ambasada Mansur Nuhu Bamalli ya rasu.
SOLACEBASE ta tattaro cewa Mansur Bamalli, kanin Sarkin Zazzau Amb Ahmad Nuhu Bamalli ya rasu ne a safiyar Juma’a yana da shekaru 53 a duniya.
A family source told SOLACEBASE that Magaji Garin Zazzau died in Lagos, due to ill health.
An tattaro cewa yana kan hanyarsa ta zuwa Morroco a makon da ya gabata lokacin da ya kamu da rashin lafiya.
Idan za a iya tunawa, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da nadin Mansur Nuhu Bamalli a matsayin jakada a wurin, a watan Oktoban 2022. A halin yanzu shi ne mukaddashin jakada a Morroco.
SOLACEBASE ta tattaro cewa ana shirin kai gawar zuwa Zaria