Tallafi: Biliyan N4.4bn ne kacal tazo hannu daga cikin Biliyan 13.1 da aka bawa wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a Maiduguri – Gwamnatin Borno
A ranar Litinin din da ta gabata ne gwamnatin jihar Borno ta ce Naira biliyan 4.4 ne kawai daga cikin tallafin Naira biliyan 13.1 da aka ware wa wadanda ambaliyar ta shafa a Maiduguri tazo hannu.
Kwamishinan Yada Labarai da Tsaro na Cikin Gida, Farfesa Usman Tar ne ya bayyana haka a Maiduguri yayin da yake bayar da karin haske a dakin taro na Gwamnatin Jihar Borno.
Tar ya ce kudaden da ake da su an mika su ga sabon kwamitin bayar da agajin gaggawa da aka kaddamar wanda ya kunshi mutane masu gaskiya domin rabawa wadanda abin ya shafa.
A cewarsa, wadanda abin ya shafa da suka samu kayan abinci da tallafin kudi da za su yi tsawon makonni biyu ya kamata su yi tsammanin wani kunshin tallafi.
Kwamishinan ya ce da dama daga cikin wadanda abin ya shafa, musamman wadanda suka samu kudi da abinci a sansanonin sun koma gida, sabanin ikirarin cewa an tilasta musu barin sansanin.
Ya ce babu wanda aka tilastawa barin sansanin, ko kuma tilastawa zama, idan har yana son komawa gida, ganin cewa ruwan ya ja a mafi yawan yankunan birnin.
Ya ce gwamnati ta yi niyyar hade wasu sansanonin.











































