Tinubu Ya janye Nadin Shugaban FERMA

President Bola Tinubu signs
President Bola Tinubu signs

Shugaban kasa Bola Tinubu ya bayar da umarnin janye sunan Imam Kashim Imam don zama shugaban kwamitin gudanarwa na hukumar kula da tituna ta tarayya (FERMA).

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Cif Ajuri Ngelale, mashawarcin shugaban kasa na musamman kan harkokin yada labarai ya fitar ranar Alhamis a Abuja.

Ngelale ya ce janyewar ba zai shafi sauran nade-naden mukamai a hukumar gudanarwar FERMA ba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here